Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeKotu ta yanke wa tsohon firaminstan Koriya ta Kudu hukuncin ɗaurin shekara...

Kotu ta yanke wa tsohon firaminstan Koriya ta Kudu hukuncin ɗaurin shekara 23

Wata kotu a Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu, ta yanke wa tsohon firaministan ƙasar, Han Duck-Soo, hukuncin zaman gidan yari na shekaru 23 saboda hannu a ayyukan tayar da tarzoma.

Laifukan da ake tuhumarsa da su sun shafi ƙoƙarinsa na ayyana dokar soji a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Yoon Suk Yeol a Disamban 2024, wanda bai samu tasiri ba.

Wani alkali ya bayyana cewa an gurfanar da tsohon firaminstan ne saboda ya gaza gudanar da taron yan majalisa da ya kamata a yi kafin a ayyana dokar soji karkashin tsarin mulki.

Han Duck-Soo ya rike mukamin shugaban riƙo na Koriya ta Kudu na tsawon makonni bayan tsige Yoon.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments