Wasu ‘yan siyasar Kano masu biyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso ba su halarci taron da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya a Kano ba.
A yayin taron dai ba a ga masu biyayya ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ba a lokacin da Abba Kabir Yusuf ya bayyana a bainar jama’a karon farko bayan bullar rade-radin cewa yana duba yiwuwar sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya shafe sama da mako guda ba tare da fitowa bainar jama’a ba, inda ake cewa yana Abuja a tsawon wannan lokaci.
Rahotanni sun bayyana cewa fitowarsa ta zo ne a wajen bikin kammala karatu da raba kayayyakin tallafi ga matasa 2,260 daga cibiyoyin koyon sana’o’i na gwamnati.
Taron da Abba Kabir ya shirya a Kano a karon farko bayan fara maganar sauya sheka daga NNPP zuwa APC, Abba Kabir ya gudanar da taron raba tallafi a dandalin Open Space Theatre da ke Gidan Gwamnati, Kano.
Wadanda suka amfana sun fito ne daga cibiyoyi daban-daban da suka haɗa da Cibiyar Fina-finai, Cibiyar Kiwon Kaji, Cibiyar Kiwo, Cibiyar Tuki, Cibiyar Kiwon Kifi, Cibiyar Noma da Shuke-shuke, da sauransu.
Fitowar gwamnan dai ta ja hankalin jama’a ne saboda ita ce karon farko tun bayan fara rade-radin sauya sheƙarsa, lamarin da ya haifar da fassarori game da siyasa tsakanin magoya bayan jam’iyyar NNPP da APC.