Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTrump ya buƙaci yan Amurka su gaggauta ficewa daga Venezuela

Trump ya buƙaci yan Amurka su gaggauta ficewa daga Venezuela

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga ƴan ƙasar da ke Venezueala da su gaggauta ficewa daga ƙasar .

Matakin na zuwa ne bayan da ma’aikatar ta ce ta samu rahotonnin yunƙurin wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na tare wasu hanyoyi a ƙasar tare da duba motocin Amurkawa da na mutanen ƙasashen da ke goyon bayan Amurka.

Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan da sojojin Amurka suka kai hari ƙasar tare da da kama shugaban ƙasar, Nicolas Maduro tare da matarsa, inda suka tafi da su Amurka, tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Shugaba Trump na Amurka ya ce a yanzu ƙasarsa ce ke juya akalar ƙasar tare da haɗin gwiwar gwamnatin rikon ƙwarya.

Sai dai har yanzu makusantan Maduro ne ke iko da jami’an tsaron ƙasar.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments