Wani sabon faɗa ya ɓarke a birnin Aleppo na Syria, tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan Kurdawa, lamarin da ya tilastawa dubban fararen hula fice wa daga yankin, yayin da mutane 4 suka rasa rayukansu.
Sabon rikicin, wanda ɓangarorin biyu ke zargin juna da assasa shi, ya ƙara fito da yadda aka gaza samun daidaito tsakanin dakarun Syria da mayaƙan Kurdawan da suka ƙi amincewa da mubaya’a ga gwamnatin Damascus.
A ranar Talata da rikicin ya soma, an kashe aƙalla mutane 6 cikinsu har da mata biyu da yaro guda, a wata musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu da ke rikici da juna.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, bayan rikicin ya ɗan lafa da tsakar dare, an wayi garin ranar Laraba da ta’azzararsa.
Gwamnatin Syria ta buɗe hanya don bai wa fararen hula damar fice wa daga birnin Aleppo zuwa yankunan da ke maƙota da shi domin samun mafaka.
Majiyoyi daga gwamnatin sun sanar cewa, ya zuwa yanzu aƙalla fararen hula 10,000 ne suka fice daga yankin saboda tsanantar rikicin.