Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ya gabatar da Naira Tiriliyan 58.47.
A kasafin, Tinubu ya tsara kashe Naira tiriliyan 15.25 domin gudanar ayyukan yau da kullum na gwamnati, sannan ya ware Naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da manyan ayyuka da more rayuwa a ƙasar.
Tinubu ya tsara kasafin ne a bisa hasashen farashin gangar ɗanyen man fetur a kan Dala 64.85.
Haka an yi hasashen sama da gangar ɗanyen man fetur miliyan 1.84 a kullum, sannan ya ayyana canjin Dala a kan Naira 1,400.