Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeNa shirya tsaf domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine - Putin

Na shirya tsaf domin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine – Putin

Shugaban kasar Rasha Putin ya bayyana cewa a shirye yake domin kawo karshen yakin da ya addabi Ukraine

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa ƙasarsa ta shirya kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine, duk da cewa bai nuna alamar sassauci a kan batun ba.

A cikin jawabin sa a farkon shirin talabijin na shekara-shekara da yake yi, Putin ya ce Rasha na ganin wasu alamun cewa birnin Kyiv na nuna sha’awar shiga tattaunawa domin kawo maslaha.

Sai dai, shugaban ya jaddada cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma za ta kasance bisa sharuddan Rasha, da kuma sharaɗin cewa an magance tushen rikicin gaba ɗaya.

A yayin jawabin, Putin ya yaba da ci gaban sojojin Rasha a fagen daga, inda ya ce suna amfani da dabaru masu ƙwari duk da cewa dakarun ƙasar na fuskantar turjiya a fagen fama.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments