Hukumar raya ƙasashen Faransa AFD ta tabbatar da cewa ta yi amfani da kuɗin da ta tsara kashewa wajen gudanar da ayyukanta a shekarar 2025 da muke bankwana da ita, amma ta rage yawan kuɗin da take kashewa a Afrika.
Cikin rahotan shekara-shekara da ta saba fitar wa kan ayyukanta, hukumar AFD ta ce ta kashe kusan Yuro biliyan 14 a kan ayyukan 4,300 dake ci gaba da gudana a wannan shekara ta 2025.
Sai dai hukumar ta ce an samu raguwa a ayyukan da take gudanarwa a Afrika, saboda rashin samun isassun kuɗI.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar ke shirin rage yawan tallafin da take bayarwa saboda yadda take fuskantar barazanar ƙarancin kuɗIn da take buƙata daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutanen dake bata tallafi.
Rahotan ya kuma bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, hukumar ta rage kasafin kuɗinta da Yuro Biliyan 2.
Haka zalika, hukumar raya ƙasashe ta Faransa ta tsara kashe Yuro miliyan 700 domin gudanar da ayyukanta na shekara mai zuwa ta 2026, a wani yanayi da take fatan samun kuɗi daga ƙungiyar Tarayyar Turai da kuma attajiran dake bayar da tallafi.