Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta ba da umarnin buɗe makarantun Unity a fadin ƙasar

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin buɗe makarantun Unity a fadin ƙasar

Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin bude dukkanin makarantun Unity 47

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin buɗe ilahirin makarantun Unity 47 mallakinta da ke sassan jihohin ƙasar, waɗanda ta rufe a farkon watan nan sakamakon matsalolin tsaro da suka ta’azzara suke kuma barazana ga ɗaliban da ke makarantu.

Ma’aikatar Ilimi ta Najeriyar ce ta bayyana shirin buɗe makarantun a cikin wata rubutacciyar sanarwa da ta raba wa manema labarai.

Tun farko mahukuntan Najeriyar sun kulle makarantun ne sakamakon ta’azzarar sace-sace ɗalibai da ƴan bindiga suka faro a watan jiya, wanda ya kai ga sace ɗaliba 24 na sakandiren ‘yan mata a jihar Kebbi da kuma wasu fiye da 200 daga wata Sakandiren Katolika da ke Neja.

Duk da gargaɗin masanan tsaro dama tsokacin da wasu fitattu a ɓangaren na Ilimi suka yi game da illar da matakin kulle makarantun ka iya haifarwa, gwamnatin Najeriyar ta yi gaban kanta wajen kulle makarantun.

SourceRFI Hausa
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments