Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiBorno: Sojoji sun kashe fararen hula da dama 'bisa kuskure'

Borno: Sojoji sun kashe fararen hula da dama ‘bisa kuskure’

Harin sojin Najeriya bisa kuskure ya yi sanadin kashe fararan hula

Wasu bayanai daga jihar Borno ta yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun ce, hare-haren sojin ƙasar da suka nufi kai wa kan ƴan ta’addan da ke ɓoye a yankin ya yi sanadin kisan ɗimbin fararen hula.

Bayanan da jaridar Premium Times da wasu jaridun Najeriyar suka wallafa sun ce an kai hare-haren ne a ranar 14 ga watan nan can a Mararraba da ke ƙaramar hukumar Kukawa.

Jaridar ta ce sojojin sun yi kuskuren luguden wuta kan Masunta da direbobin motocin hanyar da ke dakon kifi wanda ya sabbaba asarar ɗimbin rayuka.

Wasu mutane 3 ganau da suka tsira da rayukansu a harin, sun ce motoci aƙalla 10 hare-haren suka lalata sai dai babu cikakkun alƙaluma kan mutanen da suka rasa rayukansu kodayake da dama da suka jikkata na karɓar kulawa a babban asibitin Munguno.

Bayanai sun ce tsawon sa’o’i sojin saman na Najeriya suka shafe suna luguden wutar wanda suka faro tun da ƙarfe 6 na asubahi har zuwa 4 na yammacin ranar Asabar 14 ga watan da muke na Disamba.

Wannan kuskuren hari na zuwa ne sa’o’i bayan rundunar Sojin saman Najeriyar ta sha alwashin baiwa jama’a kariya ta hanyar kakkaɓe barazanar ƴan ta’addan a sabon sumamen da ta faro da taimakon Amurka.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments