Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKasar Burkina Faso ta tsare wani jirgin sojin Najeriya kan keta sararin...

Kasar Burkina Faso ta tsare wani jirgin sojin Najeriya kan keta sararin samaniyar ƙasar.

Gwamnatin Burkina Faso ta ce an tilasta wa wani jirgin saman sojin saman Najeriya ɗauke da sojoji 11 sauka a ƙasar a ranar Litinin bayan da aka ce ya keta sararin samaniyar ƙasarta.

Cikin wata sanarwa daga gwamnatin ƙasar ta ce jirgin sojan na ɗauke da ma’aikata biyu da fasinjoji tara a cikinsa kuma dukkansu jami’an soji ne.

Sanarwar ta ƙara da cewa, binciken da hukumomin ƙasar Burkina Faso suka gudanar ya nuna cewa jirgin ba shi da izinin shawagi a sararin samaniyar ƙasar.

Ƙungiyar AES ta yi Allah -wadai da lamarin a matsayin keta haddin kasar, tana mai cewa “ta yi suka da kakkausan murya kan keta sararin samaniyar duk wata ƙasa da ke cikin ƙungiyarta”.

Ƙungiyar, ta yi gargaɗin ɗaukar mataki kan duk wani jirgi da ya keta sararin samaniyar da duk wata ƙasa da ke yankin ba tare da izini ba.

Ya zuwa yanzu dai babu wani bayani daga rundunar sojin saman Najeriya ko gwamnatin tarayya.

SourceBBC y
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments