Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeƘasashen Musulmi sun kalubalanci Isra'ila kan shirin korar Falasɗinawa daga Gaza

Ƙasashen Musulmi sun kalubalanci Isra’ila kan shirin korar Falasɗinawa daga Gaza

Kasshen musulmi da dama sun soki Isra’il kan shirin ta na korar Falasdinawa daga Gaza

Ƙasashen Musulmi da dama sun soki shirin Isra’ila na buɗe mashigar iyakar Gaza da Masar ga Falasadinawan da ke son fita daga zirin kawai.

A cikin wata sanarwa haɗin gwiwa da Masar da wasu kasashe bakwai suka fitar, sun ce matakin tamkar wani yunkuri ne na korar Falasdinawa daga kasarsu.

Ƙasashen dai sun yi kira da a buɗe mashigar ta kowane bangare – na shiga da kuma fita,kamar yadda shirin zaman lafiya na Shugaba Trump ya tanada.

A baya dai Isra’ila ta ce za ta yi hakan ne kawai idan aka mayar mata da gawar mutum na karshe da ya rage cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments