Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaAkpabio ya maka Natasha a kotun koli

Akpabio ya maka Natasha a kotun koli

Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha a kotun koli.

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke dangane da dakatar da ita.

Matakin Akpabio na shiga shari’ar da kansa ya kara jan hankalin jama’a, musamman ganin yadda rikicin siyasa tsakaninsa da Sanatar ya dade yana ci gaba.

Takardun kotu da aka sanya wa kwanan wata 1, Disamba, 2025, sun tabbatar da cewa Akpabio ya shigar da kara ne bayan kotun daukaka kara ta yi watsi da takardar karar da gwamnatin tarayya ta gabatar a baya.

Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar ne bisa kura-kuran tsari da suka shafi dokokin gabatar da takardu, abin da ya tayar da muhawara a fagen shari’a.

Punch ta wallafa cewa hukuncin kotun ya zo ne a cikin rikicin shari’a da siyasa da ya dabaibaye dakatar da Natasha, lamarin da ke kara tayar da kura a majalisar dattawa da ma tsakanin jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments