Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki shirin gwamnatin tarayya na biyan ma’aikatan gwamnati tallafin sufuri na Naira 70,000 a kowane wata, yana mai cewa matakin ba zai magance matsalar tsadar rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana matsayarsa ne ta bakin daraktan yaɗa manufofin kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu.
Ya bayyana tallafin a matsayin yunƙurin rage fushin al’umma kan tsadar rayuwa.
A cewarsa, matsalar tattalin arzikin ƙasar ta shafi fannoni da dama, ciki har da sufuri, abinci, haya da makamashi, lamarin da ke ƙara tsadar gudanar da harkokin kasuwanci.
Atiku ya kuma tambayi dalilin da ya sa za a ware tallafin ga ma’aikatan gwamnati kawai, alhali ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu, ’yan kasuwa da miliyoyin mutanen da ba su da aikin yi su ma suna fuskantar matsin tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa idan ana sayar da litar fetur a kusan Naira 1,400, tallafin Naira 70,000 zai iya sayen kusan lita 50 kacal. A cewarsa, wannan adadi ba zai wadatar wajen biyan kuɗin sufuri na tsawon wata guda ba.
Atiku ya buƙaci gwamnatin tarayya ta bayyana lokacin fara biyan tallafin, waɗanda za su amfana da shi da kuma lokacin kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.
Ya kuma bayyana cewa tallafin da za a biya na tsawon watanni shida ba zai zama mafita ta dindindin ga matsalar tsadar rayuwa ba.