Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiMinista Matawalle ya duba wurin gina sabuwar kwalejin likitancin sojoji a Lagos

Minista Matawalle ya duba wurin gina sabuwar kwalejin likitancin sojoji a Lagos

Ƙaramin Ministan Tsaro na Najeriya, Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya ziyarci wurin da ake shirin kafa sabuwar Kwalejin Likitanci da Kimiyyar Lafiya ta Rundunar Sojin Najeriya (AFCOM-HS), da ke Yaba, Jihar Lagos.

Matawalle ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen inganta horar da jami’an lafiya na sojoji, tare da tabbatar da cewa an kammala aikin bisa ƙa’idoji da wa’adin da aka tsara.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar ranar Litinin, ministan ya kuma bayyana cewa ya ziyarci Asibitin Sojojin Najeriya na 68 da ke Yaba.

A yayin ziyarar, Matawalle ya duba ɗakin gwaje-gwajen cututtuka da kuma shirye-shiryen asibitin na gano cutar Ebola da sauran cututtuka masu saurin yaɗuwa.

Ministan ya jaddada muhimmancin yin gwaje-gwajen lafiya domin gano cututtuka da wuri da kuma ɗaukar matakan da suka dace don hana yaɗuwarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments