Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiUba Sani: APC na samar da ci gaba a Arewa a fannonin...

Uba Sani: APC na samar da ci gaba a Arewa a fannonin Ilimi, tsaro da ababen more rayuwa

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa Arewacin Najeriya na samun ci gaba a fannonin ilimi, tsaro da ababen more rayuwa ƙarƙashin jagorancin jam’iyyar APC.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce jam’iyyar APC na ci gaba da gudanar da ayyukanta na siyasa tare da fita yaƙin neman zaɓe domin nuna wa al’umma ayyukan da ta aiwatar.

A cewarsa, APC na fita kamfen ne saboda tana da ayyukan da za ta gabatar wa jama’a, sabanin ’yan adawa waɗanda ya yi zargin cewa suna jira ne sai jam’iyyar ta fara kamfen kafin su mayar da martani.

Uba Sani ya kuma yi iƙirarin cewa ’yan adawa sun yi mamakin yadda dimbin jama’a suka halarci gangamin siyasar APC, yana mai cewa hakan na nuna yadda jam’iyyar ke samun goyon baya a tsakanin al’umma.

Sai dai waɗannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda ake sa ran za su fafata wajen gabatar da manufofinsu da ayyukan da suka yi wa jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments