Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta ce ta fara bincike kan wani lamari na harbe-harbe da ya yi sanadin mutuwar jami’an ’yan sanda biyu a sansanin ASCO da ke Ajaokuta, a arewacin Najeriya.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Naziru Bello Kankarofi, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta bayyana sunayen jami’an da suka mutu a matsayin Kofur Amos Yusuf da Kofur Grace Onimisi, waɗanda dukansu ke aiki a hedikwatar ’yan sanda ta shiyya da ke Ajaokuta.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Juma’a, a rukunin gidajen kwanan jami’an ’yan sandan da ke Ajaokuta.
Binciken farko ya nuna cewa Amos, wanda ya riga ya fara aikin dare, ya bar wurin aikinsa tare da bindigarsa ta aiki kirar AK-47, sannan ya nufi gidan Grace.
Ana zargin Amos da buɗe wa Grace wuta, inda ya raunata ta a ƙafa, kafaɗa da ciki, kafin daga bisani ya harbe kansa da bindigar.
Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara bincike domin gano cikakken abin da ya faru. Sai dai sanarwar da aka kawo ba ta fayyace ƙarin bayani kan sakamakon binciken ko halin da Grace take ciki ba.