Akalla mutane 20 ne aka kashe bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Binnari da ke Jihar Taraba, a arewa maso gabashin Najeriya.
Waɗanda suka tsira sun ce maharan sun buɗe wuta jim kaɗan bayan Sallar Juma’a, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyen tserewa domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin, Sa’idu Nuhu, ya ce an ƙirga gawawwaki sama da 20, yayin da ’yan sanda suka bayyana cewa sun gano gawawwaki 10 zuwa yammacin ranar Juma’a.
Shugaban al’umma, Malam Abubakar Saifullahi, ya ce maharan sun zo da babura kusan 50, kowannensu na ɗauke da mutum biyu. Sun kuma yi wa shaguna fashi tare da sace kuɗi, abinci da babura.
Ƙungiyar Amnesty International Nigeria ta yi Allah wadai da harin, tana zargin hukumomi da kasa kare al’ummomin karkara. Taraba na daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane.