Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaNDC ta ɗage rantsar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta zuwa 26 ga...

NDC ta ɗage rantsar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta zuwa 26 ga Oktoba


Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Sakataren Yaɗa Labaran Ƙasa na jam’iyyar, Osa Director, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

A cewar sanarwar, an ɗage taron ne sakamakon cunkoson jadawalin ayyukan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, wanda ke da wani muhimmin alƙawari a ƙasashen waje.

Osa Director ya nemi afuwar ’ya’yan jam’iyyar da magoya bayanta bisa sauyin ranar taron, tare da kira gare su da su ci gaba da jajircewa wajen neman nasarar Peter Obi, mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, da sauran ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

A wani lamari makamancin haka, Kwankwaso ya bayyana ranar Lahadin da ta gabata cewa NDC ba za ta janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 domin goyon bayan jam’iyyar ADC ko wata jam’iyya ba, duk da tattaunawar da ake yi kan haɗin kan ’yan adawa domin fuskantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen mai zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments