Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC-PCC ya yi watsi da martanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ga sanarwar da ya fitar a baya, yana mai bayyana martanin a matsayin wani yunƙuri na karkatar da hankali daga gazawar mulkin APC.
Kwamitin ya ce martanin ya ƙara tayar da tambayoyi kan alaƙar siyasar Kwankwaso da jam’iyyar APC da kuma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
A baya, ADC-PCC ya shawarci Kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC da Peter Obi ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta, da ya daina kai wa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, hare-hare, maimakon haka ya mayar da hankalinsa kan ganin an ɗora wa APC mai mulki alhakin gazawarta.
Kwamitin ya bayyana cewa, a matsayinsa na ɗan siyasar adawa, ya kamata Kwankwaso ya riƙa ƙalubalantar gwamnatin Tinubu kan yadda matsin tattalin arziki, rashin tsaro da kuma raguwar darajar rayuwar ’yan Najeriya ke ƙara taɓarɓarewa, maimakon ci gaba da mayar da Atiku da ADC abin hari.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ya ce martanin Kwankwaso bai taɓo ainihin abubuwan da kwamitin ya nuna damuwa a kansu ba.
A cewar ADC-PCC, Kwankwaso ya ambaci APC a taƙaice yayin kare kansa, amma ya fi mayar da hankali kan sukar ADC.
Kwamitin ya ce wannan lamari ya janyo tambayoyi game da abubuwan da Kwankwaso ya ɗauka a matsayin fifiko a matsayinsa na ɗan siyasar adawa.
“Me ya sa Sanata Kwankwaso ya mayar da ɗan takararmu abin magana, maimakon ya fuskanci APC mai mulki, wadda manufofinta suka ƙara jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali?” in ji kwamitin.
Kwamitin ya ce yunwa, rashin tsaro, tsadar man fetur, faɗuwar darajar Naira da kuma matsin tattalin arziki mai tsanani a ƙarƙashin gwamnatin APC sun fi damun ’yan Najeriya fiye da sa-in-sa ta siyasa tsakanin ’yan adawa.
Ya jaddada cewa ya kamata waɗannan manyan matsalolin ƙasa su kasance abubuwan da duk wani ɗan siyasa da ke da niyyar samar da madadin gwamnatin Tinubu zai mayar da hankali a kansu.
Haka kuma, kwamitin ya ƙalubalanci Kwankwaso da ya bayyana dalilin da ya sa hare-haren siyasar da yake kaiwa suka fi karkata ga Atiku da ADC maimakon jam’iyyar da ke mulki, wadda yake zargi da haddasa matsalolin da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.
“Don kauce wa duk wani ruɗani, ADC ba za ta bari Sanata Kwankwaso ya ɗauke hankalinta ba, kuma ba za ta taɓa bari hakan ta faru ba,” in ji kwamitin.
Da yake bayyana ADC a matsayin wata ƙaƙƙarfar jam’iyyar siyasa da ’yan Najeriya ke ƙara karɓa, ADC-PCC ta ce har yanzu tana mai da hankali kan haɗa kan ’yan ƙasa domin ceto Najeriya daga abin da ta bayyana a matsayin gazawar shugabancin APC.
Kwamitin ya kuma buƙaci Kwankwaso da ya daina amfani da hare-haren da yake kai wa ADC a matsayin hanyar neman tagomashin siyasa a wajen jam’iyyar APC mai mulki. A maimakon haka, ya ce idan Kwankwaso ya yi tarayya da manufofin siyasar APC, ya kamata ya fito fili ya nuna hakan ta hanyar haɗa kai da jam’iyyar.
ADC-PCC ya sake jaddada aniyar ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, mai mayar da hankali kan manufofinta, tare da jajircewa wajen samar wa ’yan Najeriya sahihin madadin shugabanci a babban zaɓen shekarar 2027.