Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeLokaci ya yi da Ukraine za ta samu sabon shugaba – Trump

Lokaci ya yi da Ukraine za ta samu sabon shugaba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce lokaci ya yi da Ukraine za ta samu sabon shugaban ƙasa, inda ya zargi Shugaba Volodymyr Zelenskyy da ƙin amincewa da damar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha domin kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar White House ranar Asabar, inda ya ce Zelenskyy ya samu damammaki da dama na cimma yarjejeniya amma bai yi amfani da su ba.

Maganganun Trump sun zo ne kwana guda bayan sanar da wata yarjejeniya da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, kan sassauta takunkumin da ya shafi fitar da man dizal daga Rasha, da nufin taimakawa wajen samar da mai a kasuwannin Amurka da na duniya.

Trump ya kuma zargi Ukraine da kai hare-hare kan matatun man Rasha, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen tsadar dizal.

Sai dai Zelenskyy ya soki matakin sassauta takunkumin, yana mai cewa hakan zai ƙara wa gwamnatin Moscow kuɗaɗen da za ta iya amfani da su wajen ci gaba da yaƙin.

A nasa martanin, Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andrii Sybiha, ya kare Zelenskyy, yana mai cewa shugaban na jagorantar ƙasar ne a lokacin yaƙi, kuma al’ummar Ukraine ne ke da ikon zaɓar wanda zai jagorance su.

Yayin da rashin jituwa tsakanin Washington da Kyiv ke ƙaruwa, yaƙin Rasha da Ukraine na ci gaba da haifar da asarar rayuka da lalacewar kadarori, duk da ƙoƙarin diflomasiyya na neman hanyar kawo ƙarshensa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments