Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGwamnatin Sokoto ta ɗauki matakan magance ƙarancin halartar makarantu

Gwamnatin Sokoto ta ɗauki matakan magance ƙarancin halartar makarantu

Gwamnatin Jihar Sokoto ta umarci hukumomin ilimi da su ɗauki matakan gaggawa domin magance ƙarancin halartar ɗalibai da malamai a wasu makarantu.

Gwamnatin Jihar Sokoto ta umarci hukumomin ilimi da su ɗauki matakan gaggawa domin magance ƙarancin halartar ɗalibai da malamai a wasu makarantu.

Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare, Farfesa Ahmad Ladan Ala, ya bayar da umarnin yayin taron duba ayyukan ma’aikatar da aka gudanar a Sokoto.

Rahotannin ƙungiyoyin sa ido da suka ziyarci makarantu sun nuna cewa wasu makarantu na fuskantar ƙarancin ɗalibai, yayin da wasu jami’an tabbatar da ingancin ilimi ba sa halartar aikin sa ido.

Kwamishinan ya umarci Daraktan Quality Assurance, Muhammad Sani Usman, da ya ɗauki matakan gyara tare da tabbatar da cewa malamai da jami’an makarantu suna bin ka’idojin halarta da sa ido.

Ya kuma buƙaci a riƙa sabunta bayanan makarantu, tare da tattaunawa da ƙungiyar shugabannin makarantun sakandare domin samar da littafin sanya hannu da zai riƙa nuna halartar malamai.

Gwamnatin ta ce za ta ƙara tsaurara sa ido kan makarantu, musamman a yayin da wasu yankunan jihar ke ci gaba da fuskantar takaita ayyukan makarantu saboda matsalolin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments