Hukumomin Saudiya sun musanta rahotannin da suka bazu a kafafen sada zumunta cewa an yi yunkurin kai harin kunar bakin wake a Masallacin Harami da ke Makka.
Hukumomin tsaron kasar sun ce an kama wani mutum ne bisa zargin takura wa masu wucewa da haddasa firgici da tsoro, ba wai saboda wani abu da ya shafi bam ko abin fashewa ba.
Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun yi ikirarin cewa mutumin yana sanye da rigar bam kuma ya kusanci Ka’aba kafin jami’an tsaro su dakatar da shi.
Sai dai Hukumar Tsaron Jama’a ta Saudiya ta ce babu gaskiya a wadannan ikirare-ikirare, inda ta tabbatar da cewa an dauki matakin gaggawa kan mutumin tare da mika lamarin ga Ofishin Masu Shigar da Kara.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiya ma ta tabbatar da cewa wanda aka kama yana cikin wadanda ake zargi da takura wa masu wucewa da haddasa firgici, ba kuma wani dan kunar bakin wake ba.