Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce kasar ta tsallake wani babban mataki na sauye-sauyen tattalin arziki, yana mai cewa yanzu lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziki da samar da wadata ga ’yan kasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi wa ’yan Najeriya a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, yayin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Shugaban ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakai masu wahala domin gyara matsalolin tattalin arzikin ƙasar, ciki har da sauye-sauyen da suka shafi tallafin man fetur da tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje.
A cewarsa, “Zamanin gyare-gyare ya yi aikinsa, yanzu kuma zamanin wadata ya fara.” Ya ce matakan da aka ɗauka sun kafa tubalin da zai ba Najeriya damar samun ci gaba mai ɗorewa.
Tinubu ya kuma ce Najeriya ta gyara alkiblar tattalin arzikinta, yana mai kira ga ’yan ƙasar da su ci gaba da haɗa kai wajen gina ƙasar.
Ya amince cewa har yanzu akwai sauran ayyuka da gwamnati ke buƙatar kammalawa, amma ya ce akwai damar samar da ƙarin ayyukan yi, inganta rayuwar jama’a da tabbatar da cewa albarkatun ƙasar sun amfani ’yan Najeriya.