Gwamnatin Jihar Kano ta amince da miƙa kwarya-kwaryar kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1 da biliyan 201, ga Majalisar Dokokin Jihar domin nazari da amincewa.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwar Jihar na 41.
A cewar Waiya, Majalisar Zartarwar ta kuma amince da ware Naira biliyan 144 da miliyan 5 domin gudanar da ayyukan more rayuwa da wasu shirye-shiryen raya jihar.
Kwamishinan ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya Kano da samar da abubuwan more rayuwa ga al’umma.
Yanzu haka, Majalisar Dokokin Jihar Kano ce za ta duba kwarya-kwaryar kasafin kuɗin, kafin ta yanke shawarar amincewa da shi.