Aƙalla mutane biyar da ke aikin haƙar ma’adinai sun mutu, yayin da wasu biyu suka jikkata bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wani wurin haƙar ma’adinai a ƙauyen Marit, Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ta Jihar Plateau.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana ranar Asabar, kamar yadda mai magana da yawun Ƙungiyar Matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar.
Wani mazaunin yankin, Simon Mundat, shi ma ya tabbatar da cewa mutane biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka. Ya bayyana cewa al’ummar yankin na cikin jimami sakamakon harin.
Mundat ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare al’ummar yankin, domin ba su damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali da tsaro.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Kakakin Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Plateau, SP Alabo Alfred, ba su fitar da martani kan lamarin ba.
A wani lamari makamancin haka a jihar, jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar ’yan banga sun fatattaki wasu da ake zargi da kasancewa ’yan ta’adda, bayan da suka kai hari a ƙauyen Latok da ke Ƙaramar Hukumar Qua’an-Pan.
Wani mazaunin yankin, Danat Noel, ya ce jami’an tsaron sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya.