Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn kashe mutane biyar a harin Boko Haram da ISWAP a Borno

An kashe mutane biyar a harin Boko Haram da ISWAP a Borno

’Yan ta’addan sun kai hari kan manoma a Wumbi, inda wani kwamandan ’yan banga da fararen hula huɗu suka rasa rayukansu.

Ana zargin ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP da kai wani mummunan hari a garin Wumbi da ke ƙaramar hukumar Kala-Balge a Jihar Borno, inda suka kashe wani kwamandan ’yan banga da fararen hula huɗu, tare da jikkata wasu da dama.

Wumbi, wata al’umma mai yawan manoma da ke kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru, ta taɓa zama babu kowa sakamakon yawaitar hare-haren ’yan ta’adda.

Sai dai a baya-bayan nan mazauna yankin sun fara komawa domin noma, ƙarƙashin kariyar kungiyar CJTF da ’yan banga.

Majiyoyi sun ce a daren Laraba ne ’yan ta’addan suka kai harin kwantan bauna da aka shirya tun da farko, inda suka zo da ɗimbin mutane musamman domin kai wa kwamandan ’yan bangan hari, wanda ya kasance babban cikas ga ayyukansu a yankin.

A lokacin harin, mafi yawan manoman sun samu damar tserewa, amma kwamandan ya tsaya domin tunkarar maharan tare da ƙoƙarin hana su ci gaba da kai hari.

Wani ɗan banga da ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce maharan sun fi kwamandan yawa, kuma daga bisani suka yi galaba a kansa bayan sun fahimci cewa harsasensu ba sa iya ratsa wasu layu da yake sanye da su. Ya ce daga nan ne suka koma suka karya masa wuya.

Lamarin ya ƙara muni lokacin da wasu mazauna yankin da jami’an tsaro suka taru domin kwashe gawar kwamandan.

Majiyar ta ce:

“Yayin da suke gab da gawar, sai aka tayar da bama-baman da aka binne a ƙarƙashin gawar kwamandan, lamarin da ya kashe wasu mutane huɗu tare da jikkata wasu daga cikin ’yan banga, CJTF da fararen hula marasa laifi.”

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, ASP Kenneth Daso, wanda ya ce kwamandan ’yan bangan da wasu mutane huɗu sun rasa rayukansu a arangamar da suka yi da ’yan ta’addan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments