Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiDangote ya zargi NMPDRA da cin hanci da zagon ƙasa

Dangote ya zargi NMPDRA da cin hanci da zagon ƙasa

Aliko Dangote ya zargi NMPDRA da zagon kasa da kuma cin hanci da rashawa.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ya zargi Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur ta Najeriya, NMDPRA da daƙile matatun man fetur na cikin gida ta hanyar yi musu zagon ƙasa.

Ya bayyana haka a wajen wani taron menama labarai, inda a ciki ya zargi hukumar da daƙile ayyukan matatun na cikin gida da hana su rawar gaban hantsi, sannan ya zargi hukumar da shugabanta da cin hanci da rashawa.

Dangote ya kuma yi zargin cewa kuɗin da shugaban hukumar Farouk Ahmed ke kashewa sun yi yawa, inda ya ce sun fi ƙarfin abin da ma’aikacin gwamnati ya ke samu, wanda a cewarsa hakan zai janyo rashin yarda da aminci daga ɓangaren ƴan ƙasa.

A baya dai hukumar ta zargi matatar man fetur ta Dangote da yunƙurin rufe kowa ta hanyar yin kaka-gida a ɓangaren harkar man fetur, sannan ta ce man da matatar za ta riƙa fitarwa ba zai wadatar da ƴan Najeriya ba.

An samar da matatar Dangote – wacce za ta iya tace ganga 650 a kullum – domin tacewa da sayar da man fetur a Najeriya a farashin Naira.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments