Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiZa a hukunta duk mai hannu a mutuwar masu hakar ma'adanai a...

Za a hukunta duk mai hannu a mutuwar masu hakar ma’adanai a jihar Neja – Gwamnatin Tinubu

An fara bincike kan mutuwar mutane 37 da suka rasu a hannun NSCDC a Jihar Neja.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ba za ta kare duk wani jami’i ko mutum da aka samu da hannu a mutuwar wasu da ake zargin masu hakar ma’adinai ba, wadanda suka rasu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya mika ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga gwamnatin Jihar Neja, al’ummar Wushishi da iyalan mutanen da suka mutu.

An kama mutanen ne a yayin wani samame da jami’an NSCDC suka gudanar domin dakile ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankin Wushishi/Lukoto na jihar.

Mohammed Idris ya ce yanayin da mutanen suka mutu na bukatar cikakken bincike mai zurfi, na gaskiya da kuma ba tare da nuna son kai ba, domin gano hakikanin abin da ya faru kafin a tantance wadanda ke da alhaki.

Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yi wani yunkuri na kare duk wanda bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu a lamarin ba.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin tarayya na kallon kare rayukan ’yan Najeriya, mutuncinsu da hakkokinsu na asali a matsayin babban nauyi da ke kanta.

Ya ce an dauki matakan gaggawa domin gano musabbabin mutuwar mutanen, bayan da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye.

Tunji-Ojo ya kuma bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Idris ya ce matakin da ministan harkokin cikin gidan ya dauka cikin gaggawa ya nuna muhimmancin da gwamnatin tarayya ke bai wa lamarin, tare da tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za a dauki matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ci gaba da yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da sauran ayyukan da suka saba wa doka, wadanda ke barazana ga tsaron kasa, albarkatun tattalin arziki da muhalli.

Sai dai ministan ya jaddada cewa dole ne jami’an tsaro su gudanar da ayyukan tabbatar da doka cikin bin ka’idojin doka tare da mutunta rayuka da mutuncin bil’adama.

Mutanen sun mutu ne bayan an kama su a yayin samamen da NSCDC ta gudanar a wasu sassan Jihar Neja tsakanin 15 da 16 ga watan Satumban 2026.

Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya tabbatar da cewa mutane 37 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne suka mutu a hannun NSCDC.

A halin yanzu ana gudanar da gwaje-gwajen kwararru, binciken likitoci da kuma gwajin gawarwaki domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwarsu.

Haka kuma, NSCDC ta kafa kwamitin bincike domin duba yanayin mutanen a lokacin da aka kama su, tsawon lokacin da suka yi a tsare, yanayin wurin da aka tsare su da kuma irin kulawar lafiya da aka ba su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments