Saturday, October 17, 2026
HomeLabarai’Yan sandan Katsina sun kama matashi kan zargin shirya garkuwa da kakansa

’Yan sandan Katsina sun kama matashi kan zargin shirya garkuwa da kakansa

Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta ce ta kama wani matashi mai shekaru 22, Sani Dikko, bisa zargin haɗa baki da wasu mutane biyu wajen sace kakansa tare da karɓar kuɗin fansa har Naira miliyan uku.

An kama Dikko tare da Kabir Sani da Salisu Bello, dukkaninsu ’yan shekara 22, a yankin Marabar Shema da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma.

Rundunar ta ce an kama su ne a ranar 12 ga Satumba, 2026, yayin wani samame da jami’an sashen yaƙi da manyan laifuka suka gudanar bisa bayanan sirri.

Kakakin rundunar ’yan sandan Katsina, DSP Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa Sani Dikko ya amsa zargin cewa shi da sauran mutanen biyu sun shirya garkuwa da kakansa, Alhaji Lawal, kimanin makonni uku kafin kama su.

A cewar rundunar, Lawal ya shafe kwanaki 16 a hannun masu garkuwa da shi kafin a sake shi bayan an biya Naira miliyan uku a matsayin fansa.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike yayin da mutanen ukun ke tsare domin gano ƙarin bayanai da kuma tantance yiwuwar akwai wasu mutane da ke da hannu a lamarin.

A wani samame na daban, ’yan sandan sun kuma ceto wasu mata biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙauyen Sha’iskawa Fulani da ke ƙaramar hukumar Kankia.

Rundunar ta ce ’yan bindiga kimanin takwas sun kai harin da tsakar dare ranar 14 ga Satumba, inda suka yi awon gaba da Assubi Rabe mai shekaru 45 da Rabi Isyaku mai shekaru 27.

Bayan samun rahoton lamarin, jami’an tsaro sun kai ɗauki, inda suka yi musayar wuta da maharan tare da tilasta musu tserewa zuwa daji.

Daga bisani aka samu damar ceto matan biyu cikin ƙoshin lafiya.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ali Fage, ya yaba wa jami’an bisa aikin da suka gudanar, tare da kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen dakile laifuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments