Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiASUU ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’o’i uku na jihar...

ASUU ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a jami’o’i uku na jihar Lagos

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU reshen Jihar Lagos ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani a LASU, LASUED da LASUSTECH, bayan wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnatin jihar ya ƙare ba tare da warware matsalolinta ba.

ASUU ta ce babban buƙatarta shi ne a aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta Disamba 2025, ciki har da alawus-alawus da sauran hakkokin malaman jami’a. Ta ce yajin aikin zai ci gaba har sai an cimma matsaya mai gamsarwa.

A Jihar Taraba kuma, ASUU ta ba gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14, daga 14 zuwa 28 ga Satumba, domin aiwatar da wasu tanade-tanaden yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta 2025.

Sai dai a Jihar Plateau, ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 26 ga Agusta, bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar kan buƙatunta guda shida. An umarci malamai su koma bakin aiki daga tsakar daren 16 ga Satumba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments