Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta gargadi jami’anta a faɗin ƙasar da su kasance cikin shiri bayan samun bayanan sirri kan yiwuwar kai hare-haren ta’addanci a makarantu, wuraren ibada, sansanonin NYSC da sauran wuraren da ake ganin suna cikin haɗari.
Rundunar ta ce ana zargin hare-haren na iya faruwa ne a daidai lokacin da ake shirin fara sabon zangon karatun shekarar 2026/2027.
A wata sanarwa da Sashen Ayyuka na rundunar ya fitar, an umarci kwamishinonin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su ƙara sintiri da sa ido, tare da gudanar da binciken ababen hawa da mutane da kuma ƙarfafa tsaro a wuraren da ake ganin za su iya fuskantar barazana.
Rundunar ta kuma ce akwai bayanan da ke nuna cewa wasu ’yan bindiga na iya yin zirga-zirga ta hanyar Katsina zuwa Kaduna da Jihar Filato, yayin da ake zargin wasu da ake dangantawa da mayaƙan ISWAP da abokan hulɗarsu na cikin gida da gudanar da bincike kan wuraren da ake shirin kai wa hari.
Hedkwatar Tsaron Najeriya ta ce tana sa ido kan lamarin, yayin da Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC) ta ƙara ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri tare da tura jami’ai na musamman domin kare makarantu.
Masana tsaro sun buƙaci jama’a da su kasance cikin faɗakarwa tare da kai rahoton duk wani mutum, abin hawa ko yunƙurin da suka yi zargin ba shi da kyau ga hukumomin tsaro.
Sun kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa tattara bayanan sirri da ɗaukar matakan kariya tun kafin faruwar hare-hare, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.
Ƙungiyar iyaye da malamai ta Najeriya ta yi kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a makarantu, tare da amfani da fasahar zamani wajen gano abubuwan da ake zargi. Ƙungiyar ta kuma buƙaci a farfaɗo da shirin Safe School Initiative domin ƙara kare makarantu.
Duk da gargaɗin, jami’an tsaro sun buƙaci iyaye da kada su bari tsoro ya hana yara komawa makaranta, suna mai cewa kare makarantu na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, makarantu, iyaye da sauran al’umma.