Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiPeter Obi: Najeriya ta koma sansanin ’yan gudun hijira

Peter Obi: Najeriya ta koma sansanin ’yan gudun hijira

Ya ce gwamnati ta gaza kare ’yan ƙasa da mayar da waɗanda rikici ya raba da gidajensu

Dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa kashe-kashe da hare-haren da ake ci gaba da kai wa a Najeriya sun daɗe suna faruwa, lamarin da ya ce ya mayar da ƙasar tamkar sansanin ’yan gudun hijira.

Obi ya ce gwamnati ta gaza isar da matakan tsaro da suka dace domin kare ’yan ƙasa da kuma mayar da mutanen da rikici ya raba da gidajensu zuwa garuruwansu.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci wata al’umma da aka kai wa hari a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Plateau, inda ya je domin jajanta wa mutanen da rikicin rashin tsaro ya raba da matsugunansu.

Obi ya ce abin da ya sa ya ziyarci yankin shi ne nuna damuwa kan halin da ’yan Najeriya da aka tilasta musu barin gidajensu ke ciki.

Ya ce dole ne gwamnatin tarayya ta gaggauta magance matsalar kashe-kashe da garkuwa da mutane, wadanda ke tilasta wa al’ummomi barin gidajensu a sassan ƙasar, musamman a jihohin Plateau da Benue.

“Matukar kuna sansanin ’yan gudun hijira, to Najeriya ma sansanin ’yan gudun hijira. Sai kun koma gida ne Najeriya za ta koma gida. Bai kamata ku kasance a nan ba,” in ji Obi.

Ya yi kira ga gwamnati da ta fi mayar da hankali kan matsalar tsaro tare da ɗaukar kwararan matakan hukunta waɗanda ke kai hare-hare kan ’yan ƙasa marasa laifi.

Obi ya amince cewa addu’a na da muhimmanci wajen neman mafita ga matsalolin tsaro, amma ya jaddada cewa gwamnati ce ke da alhakin kare rayukan ’yan ƙasa da kuma dakile masu aikata laifukan.

“Na ji wani yana cewa muna buƙatar addu’a. Eh, muna buƙatar addu’a. Amma gwamnati ce za ta iya magance wannan matsalar. Mutanen da suke zuwa suna kashe mutane ba daga wata ba ne. Mun san su. Ya kamata gwamnatin Najeriya ta iya magance wannan matsala,” in ji shi.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ya shafi yara, yana mai cewa rushewar al’ummomi ta tilasta wa yara da dama barin makaranta.

Obi ya ce lamarin na matuƙar tayar da hankali musamman idan aka yi la’akari da yawan mutanen da abin ya shafa, inda ya ce kusan mutane 45,000 daga al’ummomi sama da 20 ne aka raba da matsugunansu.

“Ku yi tunanin mutane 45,000 a wuri guda, daga al’ummomi sama da 20. Wannan abin da ba za a amince da shi ba ne. Abu ne da bai kamata mu bari ya ci gaba da faruwa ba,” in ji shi.

Ya ce yana fatan sauran mutanen da ke neman zama shugaban ƙasar za su ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira a faɗin Najeriya domin su ga halin da ’yan ƙasar da rikici ya raba da gidajensu ke ciki.

A cewarsa, yawan ziyarar da yake kai wa al’ummomin da rikici ya shafa na da nufin jawo hankalin jama’a kan mummunan tasirin rashin tsaro ta fuskar jinƙai da rayuwar jama’a.

“Wannan shi ne karo na uku da nake zuwa nan domin faɗin abin da ke faruwa a nan. Na samu damar zuwa nan na gina makarantarku, na samar da ruwa da sauran abubuwa,” in ji shi.

Obi ya jaddada cewa ziyarar tasa ba ta da nasaba da yaƙin neman zaɓe, sai dai domin tabbatar wa mutanen sansanin cewa yana tunaninsu, kuma yana fatan za su samu damar komawa gidajensu nan gaba.

Ya kuma tabbatar wa shugabannin sansanin cewa ba su kaɗai ba ne, tare da alƙawarin ci gaba da taimaka musu gwargwadon ikonsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments