Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa shi ne zai lashe zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027 da gagarumin rinjaye.
Pantami ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa.
Ya ce yana da cikakken yaƙinin samun nasara a zaɓen, tare da bayyana cewa yana da manufofi da tsare-tsaren da zai gabatar domin samun goyon bayan al’ummar Jihar Gombe.