Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Adamu Musa, mai shekaru 35, bisa zargin basaja a matsayin babban jami’in ’yan sanda da kuma damfarar jama’a.
An kama Musa, wanda ke zaune a unguwar Kureken Sani da ke Kano, bayan rundunar ta samu rahoton neman agaji daga rundunar Police Mobile Force (PMF) da ke Challawa a ranar 1 ga Satumba, 2026.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama mutumin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
’Yan sandan sun ce jami’an sashen ’yan sanda na Panshekara sun kama Musa ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa yana gabatar da kansa a matsayin Chief Superintendent of Police (CSP).
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya kware wajen damfarar mutanen da ba su san abin da yake yi ba, ta hanyar gabatar da kansa a matsayin babban jami’in ’yan sanda mai iko a harkokin ɗaukar ma’aikata da sauya wuraren aiki.