Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro'Dan takarar gwamna a NDC ya bukaci Musulman Kano su ƙara addu’a...

‘Dan takarar gwamna a NDC ya bukaci Musulman Kano su ƙara addu’a kan matsalar tsaro

Gwarzo ya yi kira ga zaman lafiya, haɗin kai da zaman tare yayin bikin Takutaha

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NDC, Kwarmred Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bukaci Musulman jihar da su ƙara yawaita addu’o’i domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.

Gwarzo ya yi wannan kiran ne a cikin saƙon taya murna da mai magana da yawunsa, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar a ranar Talata domin taya Musulmi murnar bikin Takutaha, wanda ake gudanarwa domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Ya taya al’ummar Musulmi a faɗin Kano murnar wannan rana, inda ya bayyana Takutaha a matsayin muhimmin lokaci da ya kamata Musulmi su yi tunani kan rayuwa, koyarwa da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW).

A cewarsa, bikin ya kamata ya zama abin tunatarwa ga Musulmi game da koyarwar Annabi SAW kan zaman lafiya, tausayi, adalci, haɗin kai da zaman tare cikin lumana.

Gwarzo, ya kuma yi kira ga Musulmi da su yi amfani da bikin wajen ƙarfafa imaninsu, ƙulla zumunci da kuma inganta haƙuri da fahimtar juna tsakanin al’umma.

Ya bukaci al’ummar Musulmi da su mayar da hankali wajen yi wa al’ummomin da matsalar rashin tsaro ta shafa addu’a, musamman yankunan da ke iyaka da wasu ƙananan hukumomin jihar Kano.

Gwarzo ya ce samar da zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar haɗin kan jama’a da kuma ci gaba da addu’o’i, tare da kira ga al’ummar Kano da su riƙe darajojin soyayya, adalci, mutunta juna da zaman tare cikin lumana.

Ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, ci gaba da albarkar Allah ga jihar Kano da Najeriya, tare da roƙon Musulmi da su ci gaba da yi wa ƙasar addu’a domin samun kwanciyar hankali da ci gaba.

Ɗan takarar na NDC ya ƙara tabbatar wa al’ummar Kano cewa, idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a shekarar 2027, zai yi aiki wajen inganta shugabanci nagari, riƙon amana, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments