Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiMajalisar Shari’a ta bukaci a tabbatar wa El-Rufai adalci

Majalisar Shari’a ta bukaci a tabbatar wa El-Rufai adalci

Majalisar kolin Shari’a ta Najeriya (SCSN) ta bayyana damuwarta kan yadda ake ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, tana mai kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an bi matakan doka wajen gudanar da shari’ar.

Sakatare-Janar na majalisar, Malam Nafiu Baba Ahmad, ya ce kamar kowane ɗan Najeriya, El-Rufai yana da ’yancin a ɗauke shi a matsayin wanda ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar da aikata laifi.

Ya jaddada cewa doka ya kamata ta yi aiki kan kowa ba tare da la’akari da matsayinsa, siyasa ko wata akida ba.

Majalisar ta ce tsarin mulkin dimokuraɗiyya ya tanadi cewa kowane ɗan ƙasa yana da haƙƙin samun adalci da kuma damar kare kansa a gaban kotu.

A cewar SCSN, hukumomin da ke gudanar da shari’ar El-Rufai ya kamata su tabbatar da cewa an saurari dukkan ɓangarorin tare da bin ƙa’idojin doka, domin kauce wa duk wani zato cewa ana amfani da shari’ar ne saboda dalilan siyasa.

Zarge-zargen da ake yi wa El-Rufai

Hukumar ICPC na zargin tsohon gwamnan da aikata wasu laifuffuka da suka shafi kwangiloli, zargin karkatar da kuɗaɗe, wanke kuɗaɗen haram da kuma cin amanar ofis.

Haka kuma, Hukumar DSS na da wata shari’a da ta shafi El-Rufai kan zargin yin kutse a wayar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu.

Sai dai waɗannan zarge-zarge ne da ake gabatarwa a gaban kotu, kuma El-Rufai yana da haƙƙin kare kansa har sai an yanke hukunci.

SCSN ta bayyana cewa ba ta goyon bayan aikata laifi ko karya doka, amma ta jaddada cewa wajibi ne a tabbatar da adalci wajen gudanar da shari’ar.

Majalisar ta kuma yi gargadin cewa rashin bin matakan doka yadda ya kamata na iya jefa mutuncin hukumomin ƙasa cikin shakku.

A baya, an taɓa sakin El-Rufai na ɗan lokaci daga hannun ICPC bayan rasuwar mahaifiyarsa, amma daga bisani ya sake komawa hannun hukumomin gwamnati.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments