Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NDC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, Muhammadu Rabiu Bakinzuwo, ya bayyana goyon bayansa ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Bakinzuwo, wanda ke cikin jam’iyyar NDC da Peter Obi ke takara a ƙarƙashinta, ya ce ya fi karkata ga Atiku ne saboda alkawarin da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027.
Da yake magana a wata hira da Hantsi TV, Bakinzuwo ya soki Peter Obi kan matsayinsa na goyon bayan cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ƙara jefa talakawan Najeriya cikin tsadar rayuwa.
A cewarsa, matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta ya sa mutane ke ƙara kallon alkawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur a matsayin wata hanyar samun sauƙin rayuwa.
Bakinzuwo ya kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana zarginta da ƙara jefa jama’a cikin ƙuncin rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur, ƙarin haraji da kuma wasu ƙarin kuɗaɗen ayyuka.
Ya ambaci ƙarin kuɗin lantarki, farashin iskar gas na girki da kuma kuɗin sadarwa a matsayin wasu daga cikin abubuwan da suka ƙara wa ’yan Najeriya nauyi.
Bakinzuwo ya nuna cewa ba ya ɗaukar kasancewarsa a jam’iyyar NDC a matsayin abin da ba za a iya canzawa ba, yana mai cewa “NDC ba Alƙur’ani ba ce”, saboda haka zai iya sauya sheƙa idan ya ga wani ɗan takara da ya fi dacewa da ra’ayinsa.
Duk da kasancewarsa babban jami’i a NDC, ya ci gaba da yabon Atiku tare da nuna cewa alkawarin dawo da tallafin man fetur ya dace da abin da yake ganin zai taimaka wa talakawa.
Atiku, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya sha alwashin dawo da wani tsarin tallafin man fetur idan ya samu nasara a zaɓen 2027.
A gefe guda kuma, Peter Obi ya kasance cikin ’yan siyasar da suka nuna goyon baya ga cire tallafin man fetur, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ke raba ra’ayin ’yan siyasa yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa.