’Yan bindiga sun kai hari garin Rantan da ke ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wata mata.
Dagacin garin Rantan, Alhaji Muhammad Adamu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce zuwa yanzu, ’yan bindigar sun kashe mutane biyu, sannan suka yi garkuwa da matar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe.
Harin na zuwa ne kwana guda bayan ’yan bindiga sun kai farmaki garin Chiromawa, da ke makwabtaka da Rantan, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama.
Lamarin ya ƙara jawo fargaba a tsakanin mazauna yankunan, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a wasu sassan jihar Kano.