Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dr Aminu Yusuf Wushishi, ya rasu.
Rahotanni sun ce Dr Wushishi ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, watanni takwas kacal bayan ya fara jagorantar hukumar.
Marigayin ya karɓi ragamar shugabancin Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa a wani lokaci da hukumar ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da muhimman ayyukan ƙidaya da tattara bayanan jama’a.
An samu labarin rasuwarsa ne a yau, lamarin da ya jefa ma’aikata da abokan aikinsa cikin alhini.
Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma ba iyalansa da ’yan uwansa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.