Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ta buƙaci hukumomin tsaro su binciki wani bidiyo da ke nuna Sanata Francis Fadahunsi yana magana da magoya bayan jam’iyyar APC a lokacin zaɓen gwamnan jihar.
Ƙungiyar Imole Campaign Council ta ce Fadahunsi ya bayyana a wani rumfar zaɓe da ke NUD Primary School Collation Centre a Ilase-Ijesa, inda ake zargin ya umarci magoya bayansa su sanya ido kan yadda mutane ke kaɗa ƙuri’a.
A cikin bidiyon, an ji Fadahunsi yana cewa magoya bayan su “monitor their ballot”, sannan ya ƙara da cewa, “Whoever does not vote appropriately…” kafin ya ci gaba da wasu bayanai.
Kakakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen, Pelumi Olajengbesi, ya ce kalaman sun zama barazana ga ’yancin masu zaɓe na yin zaɓinsu cikin ’yanci.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya da rashin bin tsarin dimokuraɗiyya, tare da kira ga jami’an tsaro su gaggauta shiga lamarin.
Olajengbesi ya kuma tuna da kalaman da Fadahunsi ya yi a baya kan ’yan jam’iyyar Accord, inda ya yi barazanar cewa za a “kashe” ’yan jam’iyyar idan aka gan su a Ilesha, kafin daga baya ya ce kalaman nasa na nufin kayar da jam’iyyar ne ta hanyar ƙuri’a.
Ƙungiyar ta buƙaci hukumomin tsaro su binciki bidiyon tare da ɗaukar matakin da ya dace idan aka tabbatar da zargin.