Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da gano gawarwaki tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar.
Ana zargin ’yan bindiga ne suka kashe mutanen yayin da suke tafiya a kan hanyar, lamarin da ya sake jawo damuwa kan matsalar tsaro a yankin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce an tura jami’an ’yan sanda da sojoji zuwa wurin bayan samun rahoton faruwar lamarin ranar Talata.
Ya ce jami’an sun kwashe gawarwakin tare da fara gudanar da samame a yankin domin tabbatar da cewa babu wata barazana da ke ci gaba da kasancewa.
“An tura jami’an ’yan sanda da sojoji zuwa wurin, an kwashe gawarwakin, sannan aka ƙara tsaurara aikin share fagen tsaro domin tabbatar da zaman lafiyar yankin,” in ji shi.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumomin tsaro sun ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja.
Daga cikin waɗanda aka ceto, mutum 163 an sace su ne daga ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara, yayin da aka yi garkuwa da wasu 145 a wani hari daban a Jihar Neja.