Shahararren mawaƙin Najeriya na Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi kira ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da ya sanya ido kan halin da ake ciki gabanin zaɓen gwamnan Jihar Osun.
Davido ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar samun tashin hankali, barazana da kuma ƙoƙarin kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya yayin zaɓen.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, mawakin ya nemi Trump da sauran ƙasashen duniya su sa ido sosai kan zaɓen, tare da ƙarfafa hukumomin Najeriya da su tabbatar da tsaron masu kaɗa kuri’a.
Ya ce al’ummar Jihar Osun na da haƙƙin yin amfani da kuri’arsu cikin ’yanci ba tare da fargabar tsoratarwa ko tashin hankali ba.
Davido ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana, gaskiya da sahihanci, tare da mutunta zaɓin al’ummar jihar.