Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugabannin addini sun yi watsi da amfani da addini wajen tayar da...

Shugabannin addini sun yi watsi da amfani da addini wajen tayar da rikici

Shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci a Yammacin Afirka sun yi alkawarin inganta koyarwar addinansu tare da yin watsi da duk wani yunƙuri na amfani da addini wajen tayar da rikici, tashin hankali da tsattsauran ra’ayi.

Shugabannin addinin Musulunci da Kiristanci a Yammacin Afirka sun yi alkawarin inganta koyarwar addinansu tare da yin watsi da duk wani yunƙuri na amfani da addini wajen tayar da rikici, tashin hankali da tsattsauran ra’ayi.

Shugabannin sun bayyana hakan ne a cikin yarjejeniyar Abuja Accord da suka rattaba hannu a ranar Laraba, bayan kammala taron ƙasa da ƙasa na kwanaki biyu kan bambancin ra’ayi da zaman lafiya a Abuja.

Taron ya samu haɗin gwiwar Muslim World League da ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Najeriya.

A cikin sanarwar da Garbadeen Muhammed, ɗaya daga cikin kwamitin shirya taron, ya karanta, shugabannin sun ce ya zama wajibi malamai su tabbatar da cewa ba a karkatar da koyarwar addini domin ƙarfafa tashin hankali ko tsattsauran ra’ayi.

Sun ce addini saƙo ne na rahama da zaman lafiya, don haka ya kamata shugabannin addini su bayyana ingantattun koyarwarsa tare da ƙin amfani da shi wajen tabbatar da tashin hankali.

Sun kuma bayyana bambancin addini, al’adu da ƙabilu a matsayin wata dama ta ƙara fahimtar juna da bunƙasa al’umma, ba wani dalilin rarrabuwar kai ba.

Shugabannin sun jaddada muhimmancin tattaunawa tsakanin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, tare da ƙarfafa amincewa da haɗin gwiwa domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Sun kuma yi kira da a kare matasa daga koyarwar tsattsauran ra’ayi, ƙiyayya da son zuciya, tare da tabbatar da cewa wa’azin addini ya kasance bisa hikima da daidaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments