Wata kotu a Syria ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa bayan ta same shi da laifin aikata laifukan yaƙi da kuma cin zarafin bil’adama a lokacin yaƙin basasar ƙasar.
Assad bai bayyana a gaban kotun ba yayin yanke hukuncin. Wannan shi ne karon farko da aka yanke masa hukunci tun bayan hambarar da gwamnatinsa a watan Disamban 2024, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin danginsa na shekaru da dama.
Bayan hambarar da shi, Assad ya tsere daga Damascus zuwa Moscow tare da iyalansa, inda suka samu mafaka. Tun daga lokacin ne hukumomin Syria suka fara gudanar da bincike kan zarge-zargen da suka shafi mulkinsa da kuma laifukan da aka aikata a lokacin yaƙin.
Haka kuma, kotun ta yanke wa ɗan’uwan Assad, Atef Najib, hukuncin kisa. Najib, wanda ya kasance babban jami’in tsaro a lardin Deraa, ya gurfana a gaban kotun sanye da kayan gidan yari yayin da aka karanta masa hukuncin.
Deraa na da muhimmiyar rawa a tarihin rikicin Syria, domin ana kallon lardin a matsayin wurin da zanga-zangar da ta rikide zuwa yaƙin basasa kan mulkin Assad ta fara.