Tsohon Ministan Sufuri, Femi Fani-Kayode, ya soki kiran malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Jingir, na neman ci gaba da amfani da tikitin Muslim-Muslim a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jingir ya yi kira ga Musulmai da su mara wa tikitin Muslim-Muslim baya, tare da ƙarfafa su da su mallaki katin zaɓe domin shiga zaɓen da ke tafe. Ya kuma bayyana cewa ba zai sauya matsayinsa kan wannan batu ba.
Sai dai Fani-Kayode ya bayyana irin waɗannan kalamai a matsayin masu tayar da hankali, yana mai gargadin cewa amfani da addini wajen siyasa na iya haifar da rarrabuwar kawuna da jefa ƙasar cikin haɗari.
Ya ce Najeriya ƙasa ce da ke da mabiya addinai daban-daban, musamman Musulmi da Kiristoci, don haka bai kamata bambancin addini ya zama abin raba kan al’umma ba.
Fani-Kayode ya ƙara da cewa goyon bayansa ga tikitin Muslim-Muslim a zaɓen 2027 bai dogara da addinin ’yan takarar ba, sai dai cancanta, ƙwarewa, halayya da kuma damar da suke da ita wajen jagorantar ƙasar.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mayar da hankali kan manufofin ’yan takara, ƙwarewarsu da abin da za su iya kawowa ƙasar, maimakon yin siyasa bisa bambancin addini.