Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiCristiano Ronaldo da abokiyar zamansa Georgina za su ɗaura aure a mako...

Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa Georgina za su ɗaura aure a mako mai zuwa

Cristiano Ronaldo da abokiyar zamansa, Georgina Rodriguez, na shirin ɗaura aurensu a ƙarshen mako mai zuwa a tsibirin Madeira da ke ƙasar Portugal, inda fitaccen ɗan wasan ya taso tun yana yaro, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An ce za a gudanar da ɗaurin auren ne a Cocin Funchal Cathedral, ɗaya daga cikin manyan cocin tsibirin, inda ake sa ran iyalai da abokan arziki za su halarta.

Bayan an kammala ɗaurin auren, baƙi za su wuce zuwa Savoy Palace Hotel, wani kayataccen otel, domin gudanar da liyafar bikin.

Ronaldo da Georgina sun shafe shekaru tare kuma suna da yara, lamarin da ya sa magoya bayansu a faɗin duniya suka dade suna jiran sanarwar aurensu.

Sai dai har zuwa yanzu, ma’auratan ba su fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da ranar ɗaurin auren ba, duk da cewa rahotannin sun ce shirye-shiryen bikin sun yi nisa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments