Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKasafin kuɗin 2026: An ware Naira biliyan 400 domin gyaran masallatai da...

Kasafin kuɗin 2026: An ware Naira biliyan 400 domin gyaran masallatai da masarautu

Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnatin tarayya sun ware kusan Naira biliyan 400 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin ayyuka da suka haɗa da gyaran masallatai, fadodin sarakuna, dakunan taro, kasuwannin ƙauyuka da cibiyoyin al’umma.

Binciken ya nuna cewa hukumomi 78 ne suka saka irin waɗannan ayyuka a cikin kasafin, lamarin da ya jawo muhawara daga masana tattalin arziki da masu sa ido kan harkokin gwamnati.

Masana sun bayyana cewa ya kamata a fi bai wa muhimman fannoni kamar ilimi, lafiya, tsaro da samar da ayyukan yi fifiko, musamman a wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.

Sai dai gwamnati na iya bayyana cewa waɗannan ayyukan na daga cikin shirye-shiryen bunƙasa al’umma da inganta kayayyakin more rayuwa a sassa daban-daban na ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments