Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKano ta umarci ma’aikatan da aka biya albashi sau biyu su gaggauta...

Kano ta umarci ma’aikatan da aka biya albashi sau biyu su gaggauta mayar da shi

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci duk ma’aikatan da suka karɓi albashin watan Yulin 2026 sau biyu da su gaggauta mayar da ƙarin kuɗin da suka karɓa, bayan bankin da abin ya shafa ya kasa cire kuɗin kai tsaye daga asusun ma’aikatan.

A cikin wata sanarwa da Ofishin Akanta Janar ya fitar ranar 27 ga Yulin 2026, an umarci ma’aikatan da abin ya shafa su biya kuɗin zuwa asusun Kano State E-Salary Account na bankin UBA.

Sanarwar ta kuma buƙaci ma’aikatan su kai shaidar biyan kuɗin zuwa Ofishin Akanta Janar da ke Treasury House, No. 23 Commissioner Road, Kano, domin tantancewa da karɓar takardar shaidar mayar da kuɗin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments