Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi wa ma’aikatan masana’antar motoci abin alheri fiye da yadda iyayensu suka yi musu.
Trump ya yi wannan ikirari ne yayin wani taron kamfen da ya gudanar a cibiyar gwajin motocin kamfanin General Motors (GM) da ke Milford, jihar Michigan, ƙasa da kwanaki 100 kafin zaɓe a Amurka.
A jawabinsa, Trump ya kare manufofinsa kan masana’antar motoci, musamman harajin da ya kakaba kan motocin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Ya ce wannan mataki ya taimaka wajen bunƙasa samar da manyan motoci da SUV a Amurka, yana mai ikirarin cewa samarwar GM ta ƙaru da kusan kashi 20 cikin 100 a shekarar 2026.
Trump ya kuma soki shugaban ƙungiyar ma’aikatan motoci ta UAW, Shawn Fain, saboda goyon bayan da ƙungiyar ta bai wa Joe Biden da Kamala Harris a zaɓen 2024.
Ya yi zargin cewa da ‘yan Democrat sun ci gaba da mulki, masana’antar motoci ta Amurka ba za ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi ba.
Sai dai alkaluman Hukumar Kididdiga ta Ma’aikata ta Amurka sun nuna cewa yawan ma’aikatan masana’antar motoci da kayan haɗa motoci ya ragu da kusan kashi 4 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Disamban 2024, lamarin da ya ƙara jawo muhawara kan tasirin manufofin Trump ga tattalin arzikin ƙasar.