Monday, October 19, 2026
HomeTsaro'Yan bindiga sun sace ma'aikacin INEC a Anambra, ɗan kasuwa ya tsallake...

‘Yan bindiga sun sace ma’aikacin INEC a Anambra, ɗan kasuwa ya tsallake rijiya da baya

'Yan bindiga sun nemi a biya su kudin fansa na Naira miliyan 40

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani ma’aikacin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a yankin Ebenebe da ke ƙaramar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, yayin da wani ɗan kasuwa ya tsira daga wani hari daban a wannan hanya bayan ya samu raunin harbin bindiga.

Majiyoyin ‘yan sanda sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kai rahoton lamarin zuwa Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta B Division da ke Awka a ranar 25 ga Yuli.

A cewar majiyoyin, Emmanuel Nwobodo daga Nibo ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 5:45 na yammacin ranar 24 ga Yuli yana kan hanyarsa ta komawa gida daga Oba Ofemili a cikin motarsa kirar Mercedes-Benz E-Class, lokacin da wasu mutum huɗu dauke da makamai, sanye da baƙaƙen kaya, suka buɗe masa wuta a kusa da Makarantar Sakandaren Ebenebe Community.

Rahoton ya ce Nwobodo ya ci gaba da tuki duk da harbin da ake yi masa, kafin ya tsaya kusa da wata cocin Katolika da ke tazarar kilomita kaɗan daga wurin, inda ya gano cewa harsashi ya ji masa rauni a gwiwar ƙafarsa ta hagu. Motarsa ma ta samu ɓarna a na’urar sanyaya injin da kuma ɓangaren kujerar baya.

A yayin harin, ma’aikatansa Tochukwu Afunenu mai shekara 40, wanda ke riƙe da katin ATM da wayoyi biyu na Nwobodo, ya yi tsalle daga motar tare da guduwa zuwa cikin daji.

Majiyoyin ‘yan sanda sun ce daga baya Nwobodo ya fara zargin wani abu bayan an ce an aika saƙonnin murya daga wayar ma’aikacin nasa da ke ikirarin cewa an yi garkuwa da shi, tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 40.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments